Isa ga babban shafi
Najeriya-Siyasa

Sanatocin Jam'iyyar APC 15 sun sauya sheka zuwa PDP

Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki ya sanar da ficewar wasu sanatoci 15 daga Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya tare da komawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Majalisar Dattijan Najeriya.
Majalisar Dattijan Najeriya. Nigeria National Assembly
Talla

Cikin wata wasika daga mambobin majalisar su 15 da Bukola Saraki ya karanta gaban zaman majalisar ya bayyana sunayen Sanatocin irinsu, Rabi’u Musa Kwankwaso mai wakiltar Kano ta tsakiya da Dino Milaye mai wakiltar Kogi ta yamma da Adesoji Akanbi na Oyo da Monsurat Sunmonu daga Oyo ta tsakiya sai Rafi’u Ibrahim daga Kara ta kudu da kuma Sulaiman Hunkuyi daga Kaduna ta Arewa tare da Lanre Tejuoso daga Ogun ta tsakiya.

Sauran Sanatocin sun hada da Usman Nafada daga Gombe da Ibrahim Dambaba daga Sokoto sai Mohammed Shittu daga Jigawa tare da Isa Misau daga Bauchi da kuma Suleiman Nazif daga Bauchi da kuma Shaaba Lafiagi tare da Barnabas Gemade daga Benue.

A bangare guda kuma akwai Murtala Nyako daga Adamawa wanda tun farko ya sauya sheka zuwa ADC.

Matakin dai na zuwa ne bayan rigin-gimun da ita Jam'iyya mai mulki ke fuskanta wanda tun bayan bayyana aniyar shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na sake tsayawa takarar zabe a 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.