Isa ga babban shafi
Nijar

Bikin cika shekaru 58 da samun 'yanci a Nijar

A wannan juma’a Jamhuriyar Nijar na gudanar da bukukuwan cika shekaru 58 da samun ‘yancin kai, ranar da ga al’ada ake gudanar da kwarya-kwaryan biki tare da dashen itatuwa a sassa daban daban na kasar domin yaki da hamada. 

Issifou Mahamadou Shugaban Jamhuriyar Nijar
Issifou Mahamadou Shugaban Jamhuriyar Nijar ONEP-NIGER
Talla

A jawabin da ya gabatar dangane da zagayowar wannan rana, shugaba Issifou Mahamadou, ya fi mayar da hankali ne a game da matsalar tsaro da kasar ke fama da ita sakamakon kungiyoyin ta’addanci, masu fataucin miyagun kwayoyi da dai sauransu,Shugaba Issifou ya yi kira zuwa iyayen yara na su kulla da yaran su wajen zuwa makaranta.

A cikin jawabin shugaba Issifou ya yaba da jan aiki da jami’an tsaron kasar ke yi domin tabbatar da tsaro a wasu sassan kasar.

A ciki jawabin sa shugaba Issifou bai tabo zancen mutanen dake tsare ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.