Isa ga babban shafi
Najeriya

Kusan 'yan Najeriya 1500 sun mutu a hadarin mota bana- Rahoto

Wani rahoton hukumar Kididdiga ta Najeriya ya nuna cewa akalla rayukan mutane dubu daya da dari uku da talatin da daya ne su ka salwanta sanadiyyar hadarin mota a cikin watanni hudun farkon shekaran nan ta 2018.

Rahotanni na nuni da cewa galibin wadanda hadurran ya fi shafa maza ne kaso mai yawa daga cikinsu kuma masu yawan shekaru.
Rahotanni na nuni da cewa galibin wadanda hadurran ya fi shafa maza ne kaso mai yawa daga cikinsu kuma masu yawan shekaru. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Rahoton ya ce, cikin wannan adadi na ‘yan Najeriyar da suka mutu sanadiyyar hadarin mota, jimillar dubu daya da arba’in da bakwai daga cikinsu maza ne, sai kuma mata dari biyu da tamanin da hudu, yayin da saba’in da hudu ke matsayin yara kanana.

Har ila yau rahoton, ya alakanta gudun wuce kima, tukin ganganci da kuma rashin ingancin tayoyin mota a matsayin babban sanadin yawaitar hadarin motar, ya kuma bayyana cewa akwai ‘yan Najeriyar sama da dubu takwas da yanzu haka ke jinya sakamakon muggan raunukan da suka samu sanadiyyar hadarin motar a wancan wa'adi na watanni hudun farkon shekarar nan.

Haka zalika rahoton ya nuna cewa daga cikin adadin na dubu 7 da 946 da suka samu raunin kusan kashi 94 da na adadin, manyan Mutane ne sai kuma wasu 491,kwatankwacin kashi 6 na adadin da ke matsayin yara kankana.

Rahoton na hukumar kididdigar Najeriya ya nuna cewa gaba daya an samu hadarra sama da dubu biyu da dari shida a tsawon wa'adin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.