Sojin Najeriya sun kame wadanda ake zargi da kisan Janar Alkali
Rundunar Sojin Najeriya ta gabatar da mutane 13 da ta ke zargin suna da hannu wajen bacewar Janar Idris Alkali, wanda ya bata a watan Satumbar da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Kwamandan runduna ta 3 da ta gudanar da bincikem Umara Muhammed ya ce za su mikawa rundunar Yan Sanda mutanen da ake zargin domin gudanar da nasu bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamandan ya ce wadanda za’a mikawa Yan Sandan sun hada da wadanda aka samu da makamai da wadanda suka tare motar Janar Alkali da kuma wadanda suka tura ta cikin tafki.
Jami’in ya ce suna da bayanai kan wasu da ake zargin suna da hannu cikin lamarin amma kuma suka gudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu