Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

'Yan ta'adda sun hallaka yara 11 tare da sace 15 a Jamhuriyar Congo

Ma’aikatar tsaron Jamhuriyyar Democradiyyar Congo ta tabbatar da wani harin ‘yan ta’adda a tsakaddaren jiya da ya kai ga kisan mutane 11 tare da garkuwa da wasu 15 a gab da garin Beni kusa da kan iyakar kasar da Uganda.

Baya ga mutanen 11 ma'aikatar tsaron ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta ce akwai kuma wasu jami'an tsaro 2 da 'yan ta'addan suka hallaka.
Baya ga mutanen 11 ma'aikatar tsaron ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta ce akwai kuma wasu jami'an tsaro 2 da 'yan ta'addan suka hallaka. Guillaume Thibault/RFI
Talla

Babban jami’in ‘yan sanda na garin na Beni ya tabbatar da gano gawar mutanen 11 galibi kananan yara da shekarunsu bai haura 10 ba, wadanda ya ce an kashe su ne a kauyen Matete da ke arewacin garin na Beni.

Mai magana da yawun rundunar soji na yankin Kaftin Mak Hazukay ya ce maharan mambobi ne na wata kungiya da ake kira ADF mai adawa da ci gaban yankin.

Haka zalika Kaftin Hazukay ya ce baya ga mutanen 11 akwai kuma jami’ansu 2 da suka mutu sakamakon harin na tsakaddare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.