Isa ga babban shafi
MDD- Sudan ta Kudu

Sojin Sudan ta Kudu sun sace 'yan mata

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, soji da ‘yan tawayen kasar Sudan ta Kudu sun sace daruruwan mata manya da kanana cikin shekarar nan, in da suka yi musu fyade tare da tilasta musu lalata baya ga mayar da su kamar bayi.

Rahoton ya ce, ana baje kolin 'yan mata ga Sojojin Sudan don lalata da su
Rahoton ya ce, ana baje kolin 'yan mata ga Sojojin Sudan don lalata da su REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Rahoton Majalisar ya nuna cewa, cikin shekarar nan kadai ‘yan tawayen da sojin na Sudan sun sace tarin mata da yara kananan babu adadi, yayin da suke tilasta wa kananan yara shiga ayyukan ta’addanci, matan kuma su rika mayar da su bayi tare da tilasta musu lalata, in da rahoton ke cewa kawo yanzu akwai da dama daga cikin ire-iren wadannan yara a hannun bangarorin 2.

A cewar rahoton, bangarorin biyu na soji da ‘yan tawayen sun yi amfani da damar fadan da ya barke tsakanin sojoji masu biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma ‘yan tawayen da ke bangaren Riek Machar.

Rahoton wanda ya nuna cewa matakin ya saba wa dokokin kasa da kasa kan hakkin dan Adam, ya nuna cewa galibin matan da aka sace cikin shekarar nan shekarunsu bai haura 12 da haihuwa ba, yayin da Sojin kasar ke mayar da su matansu ba kuma tare da neman amincewarsu ba.

Rahoton ya bayyana cewa dakarun sojin kan je garuruwa tare da tattaro yaran mata tare da baje su gaban manyan jami’an sojin su zabi wadanda su ke so su yi wa fyade daga bisani kuma su mayar da su bayi.

Sai dai mai magana da yawun sojin kasar, Lul Ruai Koang ya musanta zargin yana mai cewa Majalisar ta nuna hujjar da ke nuna sun aikata laifin da ake zargin su don kuwa ba za su amince da duk wani rahoto a rubuce daga Geneva ko New York ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.