Mutane 47 sun mutu a hatsarin mota a Zimbabwe
Akalla mutane 47 sun rasa rayukansu bayan wasu motocin safa biyu sun yi karo da juna a tsakanin birnin Harare da garin Rusape da ke yankin Kudu maso gabashin kasar Zimbabwe.
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘Yan sanda sun tabbatar da asarar rayukan da aka samu a hatsarin na ranar Laraba.
A wani sakon Twitter da ta wallafa a shafinta na Twitter, Jaridar Herald ta kasar ta ce, ba za ta iya wallafa hotunan hatsarin ba saboda muninsu.
Ana yawan samun hattsuran motoci a Zimbabwe saboda lalacewar hanyoyi bayan kwashe tsawon shekaru ba tare da kula da su ba.
Koda dai bayanai na cewa, a kwanan nan aka gyara hanyar da hatsarin baya-bayan ya auku.
A shekarar bara, an samu mutane 43 da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota a yankin arewacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu