Isa ga babban shafi

Rundunar sojin Najeriya za ta yaye 'yan Boko Haram 155 da suka tuba

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana shirin yaye tsoffin 'ya'yan kungiyar boko haram 155 da aka kammala horar da su a Jihar Gombe wajen sauya musu tunani da kuma koya musu sana’a.

A cewar rundunar za’a mika wadannan mutane 155 ga hukumomin Jihohin da suka fito domin sake tsugunar da su.
A cewar rundunar za’a mika wadannan mutane 155 ga hukumomin Jihohin da suka fito domin sake tsugunar da su. REUTERS/Ahmed Kingimi
Talla

Shugaban cibiyar horar da tsoffin mayakan, Manjo Janar Bamidele Shafa ya ce wadannan sune rukuni na biyu na mayakan da aka horar bayan sun bayyana tubar su daga ayyukan ta’addanci.

Janar Shafa ya ce a watan Fabarairun da ya gabata, an yaye wasu 95 wadanda tuni aka sake su suka koma gidajen su.

Hafsan sojin ya ce za’a mika wadannan mutane 155 ga hukumomin Jihohin da suka fito domin sake tsugunar da su.

Wannan bikin yaye tsoffin mayakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar boko haram ta kai wani kazamin hari Jihar Barno inda ta kashe sojojin kusan 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.