Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Dole mu samu nasara kan Boko Haram - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana yakin da dakarun kasar keyi da mayakan kungiyar boko haram a matsayin wanda ya zama dole a samu nasara akai, duk da asarar rayukan da aka samu yan kwanakin da suka gabata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da dakarun tsaron kasar, yayin wani bukin soji a Najeriya ranar 13 ga watan Afrelu 2016
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da dakarun tsaron kasar, yayin wani bukin soji a Najeriya ranar 13 ga watan Afrelu 2016 STRINGER / AFP
Talla

Yayin jawabi ga taron hafsoshin sojin kasa a Maiduguri, shugaba Buhari ya ce an samu gagarumar nasara a yakin tun daga shekarar 2015 lokacin da wanann gwamnati ta hau karagar mulki, saboda haka babu dalilin da zai kauda hankalin sojojin wajen murkushe kungiyar daga doran kasa.

Buharin wanda ke ziyara a birnin Maiduguri na jihar Borno bayan hare-haren kungiyar ta Boko Haram kan dakarun Najeriyar da ya hallaka da dama a cikinsu ya ce dole ne Najeriyar ta hada karfi da makwabtanta don fatattakar burbushin mayakan na Boko Haram.

A baya-bayan nan dai kungiyar ta Boko Haram ta tsananta kai hare-hare inda a lokuta da dama ta ke hallaka sojojin kasashen na Najeriyar da Makwabtanta Nijar Kamaru da kuma Chadi, matakin da ya tilasta musu shirya wani zama na musamman don lalubo hanyoyin da za a magance matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.