Isa ga babban shafi
Togo

Tarzoma ta barke a birnin Lome na kasar Togo

A Togo ,an samu arrangama tsakanin yan sanda da yan adawa a wata zanga-zanga da ta gudana a babban birnin Kasar Lome.Ana zargin yan Sandada yi amfani da harsashe wajen tarwatsa masu zanga-zanga,wanda hakan ya janyo asarar rayukan mutane biyu da suka hada da wani yaro mai shekara 8.

Taron masu zanga-zanga a Lome na kasar Togo
Taron masu zanga-zanga a Lome na kasar Togo Matteo Fraschini KOFFI / AFP
Talla

Da jimawa Shugaban Ghana Nana akufo-Addo da takwaransa na Guinee Conakry Alpha Conde, sun yi kokarin sake ganawa da wakilan gwamnatin Faure Ngassingbe da kuma ‘yan adawa da ke fafutukar ganin an yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara kafin zabubuka masu zuwa.

Wata tawagar Cedeoa karkashin jagorancin Jean-Claude Brou ta ziyarci kasar Togo tareda ganawa da wakilan jam’iyyun adawar kasar 14, da kungiyoyin fararen hula da kuma bangaren gwamnati dangane da wannan batu. Bayanai na nuni da cewa babban abin da ke kawo cikas ga wannan tattaunawa da aka fara tun cikin watan fabarairun shi ne ko za a bai wa shugaba Faure Gnassingbe damar sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2020 ko kuma a’a.

‘Yan adawa dai na ganin cewa dole ne shugaba Gnassingbe ya sauka daga mulki karshen wa’adinsa a shekara ta 2020.

Jagoran yan adawa Jean Pierre Fabre ya bayyana cewa za su ci gaba da bijerewa gwamnatin Shugaba Faure Gnassingbe .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.