Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ta tsaida ranar bayyana mai masaukin bakin gasar AFCON

Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, ta bayyana 9 ga watan Janairu, a matsayin ranar da za ta bayyana sunan kasar da za’a baiwa damar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, Ahmad Ahmad.
Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, Ahmad Ahmad. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Shugaban hukumar ta CAF, Ahmad Ahmad ya ce a ranar 14 ga watan Disambar da muke ciki, za’a rufe karbar bukatar neman karbar bakuncin gasar daga kasashen dake nema, a ranar 25 ga watan kuma, CAF za ta tantance kasar da tafi cancantar samun damar.

Wannan sabon aiki da hukumar CAF ta fuskanta ya biyo bayan, matakin da ta dauka na kwace damar karbar bakuncin gasar cin kofin ta nahiyar Afrika da ta baiwa Kamaru bisa dalilan jan kafa wajen kammala shirye-shirye da kuma matsalolin tsaro.

A halin yanzu Kamaru za ta kabi bakuncin gasar ce a shekarar 2021.

Gasar cin kofin ta nahiyar Afrika za ta soma daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuly dake tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.