Isa ga babban shafi
Mali

Shugaban Mali ya ziyarci tsakiyar kasar dan kwantar da hankula

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita ya ziyarci kauyen Koulogon da ke tsakiyar kasar, domin janjantawa jama’a sakamakon harin da aka kai ranar 1 ga wannan wata wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 37.

Ibrahim Boubacar Keita, shugaban kasar Mali
Ibrahim Boubacar Keita, shugaban kasar Mali REUTERS/Luc Gnago
Talla

Shugaba Keita, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa an gano wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

A ranar 1 ga wannan wata ne ne wasu ‘yan bindiga da aka bayyana cewa sun fito ne daga kabilar Dogon, suka afka wa garin na Koulogon inda suka kashe ‘yan kabilar Fulani 37 tare da kona wani bangare na garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.