Isa ga babban shafi
Sudan-Zanga-Zanga

Sashen fikira na Sudan ya bukaci sakin wadanda aka kame a zanga-zanga

Sashen fikira na ma'aikatar tsaron Sudan ya bukaci sakin ilahirin mutanen da aka kame yayin zanga-zangar kasar da ke ci gaba da gudana fiye da wata guda.

Ko a yau Talata ma, tarin masu zanga-zangar sun gudanar da mabanbantan gangami a biranen Khartoum da Omdurman cike da bukatar lallai shugaba Omar al- Bashir ya sauka daga mulki
Ko a yau Talata ma, tarin masu zanga-zangar sun gudanar da mabanbantan gangami a biranen Khartoum da Omdurman cike da bukatar lallai shugaba Omar al- Bashir ya sauka daga mulki REUTERS
Talla

Sanarwar da ma'aikatar yada labaran Sudan ta fitar ta ce, shugaban sashen fikira na tsaron cikin gida a kasar Salah Ghosh ya bukaci sakin fiye da mutane dubu guda da ake zargin hukumomin tsaro sun kame yayin zanga-zangar.

Cikin wadanda kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargin an kame yayin zanga-zangar da ta shafe fiye da wata guda ana yi a Sudan har da masu fafutukar kare hakkin dan adam da kuma tarin 'yan jaridu.

Rahotanni dai na nuni da cewa fiye da mutane 30 Jami'an tsaro suka hallaka yayin zanga-zangar wadda ta barke tun bayan daukar matakin kara kudin Burodi zuwa ninki 3 da gwamnatin kasar ta yi.

Sai dai a bangare guda kungiyar Amnesty International ta ce adadin mutanen da jami'an tsaron suka hallaka sun haura 40.

Ko a yau Talata ma, tarin masu zanga-zangar sun gudanar da mabanbantan gangami a biranen Khartoum da Omdurman cike da bukatar lallai shugaba Omar al- Bashir ya sauka daga mukami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.