Isa ga babban shafi
Algeria-Bouteflika

'Yan Algeria na ci gaba da zanga-zanga duk da gargadin yiwuwar rikici

Dubban ‘yan Algeria sun sake fitowa zanga-zangar adawa da matakin shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika game da tsayawa takarar shugabancin kasar karo na 5, duk kuwa da gargadin da shugaban ya yi na yiwuwar fuskantar rikici sanadiyyar zanga-zangar wadda ke kara ta’azzara tun bayan fara ta a makonni biyu da suka gabata.

Zanga-zangar ta yau wadda ake ganin ita ce mafi girma na zuwa bayan goyon bayan da masu zanga-zangar suka samu daga kungiyar lauyoyin kasar
Zanga-zangar ta yau wadda ake ganin ita ce mafi girma na zuwa bayan goyon bayan da masu zanga-zangar suka samu daga kungiyar lauyoyin kasar RYAD KRAMDI / AFP
Talla

Zanga-zangar ta yau Juma’a wadda ke zuwa kwana guda bayan kungiyar lauyoyin kasar ta mara baya ga boren wanda ke da nufin kawo karshen shugabancin Abdelaziz Bouteflika kusan ita ce mafi girma kuma mafi tattara al’ummar kasar galibi matasa da kuma mata.

Yayin zanga-zangar, gwamnatin kasar ta girke tarin jami’an kwantar da tarzoma da kuma tankokin ruwan zafi a lungu da sako na sassan biranen kasar ciki har da Algiers babban birnin kasar, don tabbatar da an gudanar da boren cikin lumana.

Cikin sakon da shugaba Bouteflika ya aike a safiyar yau, ya ce akwai wadanda ke son amfani da damar wajen biyan bukatunsu ta hanyar haddasa hargitsi a kasar, inda al’ummar Algeria na da cikakkiyar damar bayyana ra’ayinsu game da takarar ta sa.

Shugaban na Algeria wanda yanzu haka ke fama da shanyewar barin jiki, ya ce akwai bukatar ‘yan kasar su sanya idanu wajen tabbatar da ba a yi amfani da su wajen wargaza kasar kamar yadda ya wakana a makotansu ba, inda ya ce kamata ya yi al’ummar kasar su yi amfani da damar zanga-zangar ta yau wajen murnar ranar mata ta duniya maimakon nuna kyamar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.