Sojin Nijar sun hallaka mayakan Boko Haram 33 a Diffa
Ma'aikatar tsaron Jamhuriyyar Nijar ta ce sojinta sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram 33 a wani sumame da suka kai maboyar mayakan da ke yankin kudu maso gabashin kasar da ke yankin tafkin Chadi.
Wallafawa ranar:
Ma'aikatar tsaron ta Nijar ta kuma tabbatar da kame tarin makamai da motoci daga hannun mayakan na Boko Haram, inda ta ce babu ko sojanta guda daya rasa ransa a sumamen na jiya Talata.
Cikin kayakin yakin da sojinta suka kame a cewar ma'aikatar tsaron, har motoci masu sulke wadanda sanarwar ta ce tuni sojinta suka lalata su, sai kuma babura 2 da bindigogi kirar AK47 10 da kuma makamai masu linzami baya ga harsasai kusan dubu 4 da sauran muggan makamai.
Sumamen dakarun sojin na Nijar ya zo ne bayan kisan jami'an 'yan sanda 7 a wani hari da ya kai ga kisan mayakan jihadi 38 a jihar Diffa wadda ke fama da hare-haren Boko Haram.
Kawo yanzu dai akalla mutane dubu 27 aka yi ittifakin sun mutu a jihar ta Diffa tun bayan farowar rikicin Boko Haram a shekarar 2009, kari akan 'yan mata kusan 20 da mayakan suka yi garkuwa da su cikin watan Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu