Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo-Ebola

Ebola ta kashe mutane 100 cikin mako 3 a Jamhuriyar Congo

Rahotanni daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo na cewa akalla mutane 100 sun mutu cikin kasa da mako 3 sanadiyyar cutar Ebola, matakin da ya mayar da adadin wadanda suka mutu sanadiyyar barkewar cutar ta baya-bayan nan zuwa sama da 700.

Yanzu haka an fara rigakafin cutar a yankunan karkara
Yanzu haka an fara rigakafin cutar a yankunan karkara REUTERS/Baz Ratner
Talla

Wasu bayanai da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar a yau, ya nuna cewa barkewar cutar a wannan karon yafi kowanne illar saurin yaduwa da kuma hallaka tarin jama’a.

Tuni dai ma’aikatar ta sanar da fara bayar da rigakafin cutar a yankunan karkara wanda ta ce tafi ta’azzara a can, inda ta ce kawo yanzu ta yiwa akalla mutane dubu 95 rigakafin allurar ta rVSV-Zebov da ke matsayin garkuwa ga cutar ta Ebola.

A cewar ma’aikatar lafiyar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo matakin wani yunkuri ne na kare dubban rayukan ‘yan kasar da ke cikin hadarin kamuwa da cutar ta Ebola.

Wannan dai ne karo na 10 da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke fuskantar barkewar cutar ta Ebola cikin shekaru 40.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.