Isa ga babban shafi
Mali

Gwamnatiin Mali ta yi murabus saboda kisan Fulani

Firaministan Mali da daukacin mambobin gwamnatinsa sun yi murabus daga mukamansu, makwanni hudu da kisan da aka yi wa Fulani makiyaya 160, abinda ya girgiza al’ummar kasar.

Soumeylou Boubeye Maiga
Soumeylou Boubeye Maiga MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita ya karbi takarar murabus din Firaminista, Soumeylou Boubeye Maiga da jama’arsa kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar.

Sai dai fadar ba ta yi karin bayani ba game da ajiye aikin Maiga, amma a ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Kasar ta tattauna kan yiwuwar kada kuri’ar yankar kauna kan gwamnatin Maiga saboda kisan kiyashin da aka yi wa Fulanin, yayinda kuma gwamnatinsa ta gaza wajen karbe makamai daga hannun ‘yan tawaye da mayakan jihadi.

Ana zargin mafarautan kabilar Dogon da kaddamar da farmaki kan Fulanin a kauyen Ogossagou da ke tsakiyar Mali a ranar 23 ga watan Maris da ya gabata.

Kazalika mayakan jihadi sun kai farmakin da ya kashe sojojin kasar 23, harin da kungiyar da ke da alaka da al-Qeda ta dauki alhakin kaddamarwa.

Maiga na shan suka sakacinsa na tunkarar rikicin kabilanci a Mali wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ya lakume rayukan mutane akalla 600 tun daga watan Maris na shekarar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.