Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane a yankin Morou dake Zamfara

Mutane 16 ne suka rasa rayukansu a harin da ‘yan bindiga suka kai wa garin Kanoma da ke yankin Morou a jihar Zamfaran Najeriya cikin daren jiya alhamis.

Wani asibiti dake yankin Gusau a jihar Zamfara
Wani asibiti dake yankin Gusau a jihar Zamfara AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya shaida wa manema labarai cewa yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 2 na daren laraba zuwa wayewar garin alhamis, yayin da ya ce akwai wasu mutane da dama da ke jinya sakamakon harbin su da bindiga lokacin wannan hari.

A yan watanni da suka gabata, Rundunar Sojin saman Najeriya ta ce ta na shirye shiryen aikewa da karin jirage na yaki kirar Agusta 109 zuwa jihohin Zamfara da Katsina masu fuskantar matsalar hare-haren ‘yan bindiga.

A cewar wata majiyar rundunar sojin Najeriyar za a aike da jiragen ne,a matsayin wani sabon yunkuri don kammala murkushe ‘yan bindigar da ke haifar da barazanar tsaro a jihohin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.