Isa ga babban shafi
Chadi

Deby ya dage takunkumin amfani da dandalin sada zumunta

Shugaban Chadi Idris Deby ya bayyana dage takunkumin shiga wasu shafukan yanar gizo gami dandalin sada zumunta na zamani da gwamnatinsa ta sanyawa 'yan kasar a shekarar bara saboda dalilai na tsaro.

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby.
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby. AFP
Talla

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa, dage takunkumin a yau asabar, ya baiwa yan kasar damar shiga shafukan samun labarai da kuma dandalin sada zumunta musamman na Wattsapp da Twitter.

Rahotanni sun ce a halin yanzu kasa da kashi 10 na yan Chadi ne ke iya shiga shafukan na Internet, abinda masu bibiyar lamurran kasar suka danganta da tsadar samun damar hawa dandalin shiga shafukan.

Chadi na cikin kawancen kasashen da ke yakar kungiyoyi masu da’awar Jihadi ciki harda Boko Haram, wadda a baya ta kai hare-hare cikin kasar.

Daga bangaren iyakarta da kasashen Nijar, Libya da Sudan kuwa gwamnatin ta Chadi na fama da yan tawayen kasar da suka kafa sansani, wadanda a watan Janairu da ya gabata suka yi kokarin kifar da gwamnatin Idris Deby.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.