Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari Madarounfa

'Yan bindiga da aka bayyana cewa adadinsu ya fi dari daya sun kai kari a wani gari mai suna Shirge dake yankin Madarumfa a jihar Maradin Jamhuriyar Nijar a cikin daren jiya alhamis.

Dakarun Nijar a fagen daga
Dakarun Nijar a fagen daga AFP Photo/ISSOUF SANOGO
Talla

Gwamnan jihar Zakari Oumarou ya tabbatar da mutuwar mutane akalla 5 a wannan hari, inda ya ce har zuwa safiyar yau ana cigaba da fafatawa tsakanin 'yan bindigar da kuma jami'an tsaron kasar ta Nijar.

Madarumfa yanki ne da yayi iyaka da jihohin Katsina da Zamfarar tarayyar Nigeria mai fama da 'yan bindiga.

Rahotanni daga rundunnar tsaron Nijar na bayyana cewa tuni aka aiko da jirgin saman yaki don taimakawa dakarun dake kasa, wannan yankin ya kasance wani yankin da ake satar mutane don neman kudin fansa .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.