Isa ga babban shafi

Majalisar Dattijai ta bai wa Buhari wa'adin mika sunayen ministoci

Majalisar Dattijan Najeriya ta bai wa shugaban kasar Muhammadu Buhari wa’adin kwanaki 5 don ganin ya mika mata sunayen mutanen da yake son nadawa ministoci don tafiyar da sabuwar gwamnatinsa kan wa’adin mulki zagaye na biyu da aka rantsar da shi tun a ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ng.gov.jpg
Talla

Tun bayan rantsar da shugaban da akalla watanni biyu ya gaza mikawa majalisar sunayen ministocin, ko da dai ya gudanar da wasu manyan nade-nade da basa bukatar sahalewar Majalisar.

Majalisar dai ta bukashi shugaba Buhari ya gaggauta mika mata sunayen kafin ranar 26 ga watan Yuli da za ta fara hutu wanda za ta dawo a 26 ga watan Satumba.

A cewar shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Sanata Adedayo Adeyeye, yayin wata zantawarsa da Jaridar Punch da ake wallafawa a Najeriyar, majalisar kai tsaye za ta tafi hutunta matukar fadar shugaban kasar ta gaza mika mata sunayen nan da ranar Juma’ar mako mai kamawa.

Kafin yanzu dai, Shugaban Majalisar Ahmed Lawal a makonnin da suka gabata ya bayyana cewa ba da jimawa ba shugaban zai mikowa majalisar jerin sunayen ministocin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.