Shekaru 8 bayan harin Boko Haram MDD ta bude Ofishinta a Abuja
Majalisar Dinkin Duniya ta sake bude Ofishinta da ke Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya bayan kulle shi fiye da shekaru 8 sanadiyyar wani harin kunar bakin wake a Ofishin wanda ya kai ga daukar matakin kulle shi.
Wallafawa ranar:
Harin wanda kungiyar Boko Haram ta kaddamar a Ofishin na Majalisar Dinkin Duniya ya hallaka mutane 23 nan take baya ga jikkata wasu da dama.
A tsawon shekaru 8 da suka gabata, Majalisar Dinkin Duniyar na amfani da wasu kananun gine-ginenta ne don ci gaba da harkokinta.
Cikin sanarwar da Ofishin Majalisar ya fitar ya nuna cewa yanzu haka jami’an Ofishin sun koma ayyukansu gadan-gadan a tsohon Ofishin na su mai hawa 4 a tsakiyar birnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu