Isa ga babban shafi
Somalia

Harin Al-Shebab a sansanin Sojin Somalia ya hallaka Soji 12

Mayakan Kungiyar Al Shebaab dake Somalia sun kai hari sansanin sojin kasar da ke El Salini, inda suka kashe sojoji 12, kana suka kwace wurin na wani lokaci kafin a kore su.

Wani harin kungiyar Al-Shebaab a birnin Mogadishu na Somalia.
Wani harin kungiyar Al-Shebaab a birnin Mogadishu na Somalia. REUTERS/Feisal Omar
Talla

Nur Ahmed, jami’in 'yan Sanda a yankin ya ce wani daga cikin mayakan ya fara tada bam, kafin 'yan bindigar suka kutsa kai ciki, abinda ya yi sanadiyar salwantar rayuka.

Wani hafsan soji Ismail Ali ya tabbatar da mutuwar dakarun su 12, yayin da ya bayyana cewar kwamandan sojin da ke sansanin ya samu rauni.

Mai Magana da yawun kungiyar Al Shebaab, Abdiasis Abu Musab ya ce sun kwace motoci guda biyu masu dauke da na’urar kakkabo jiragen sama, yayin da suka lalata wasu guda 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.