'Yan Algeria na bikin tuna farkon zanga-zangar hambarar da Bouteflika
Dubun dubatar mutane ne suka yi tururuwa zuwa gangamin cika shekara guda da zanga zangar da ta haifar da kawar da gwamnatin shugaba Abdelaziz Bouteflika na Algeria a birnin Algiers.
Wallafawa ranar:
Masu zanga zangar sun yi ta nuna adawar su da mulkin soji da kuma bukatar kafa gwamnatin farar hula a kasar wadda ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1962.
Ita dai zanga zangar ta barke ne ranar 22 ga watan Janairu lokacin da tsohon shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika ya bayyana aniyar sa ta yin sabuwar takara domin yin wa’adi na biyar duk da tsananin rashin lafiyar da yake fama da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu