Kasashen Sahel sun sha alwashin cigaba da barin wuta kan 'yan ta'adda
Taron kasashen dake rundunar G5 Sahel da aka yi a Mauritania ya amince da shirin ci gaba da budewa ‘yan bindiga wuta, wadanda hare-haren da suke kaiwa a cikin kasashe guda 3 na yankin yayi sanadiyar salwantar dubban rayuka da kuma karya tattalin arzikinsu.
Wallafawa ranar:
A lokacin da yake tsokaci a zaman taron da ya samu halartar kasashen Burkina Faso, Mali, Jamhuriyar Nijar da kuma Chadi, shugaban Mauritania mai masaukin baki Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani, ya ce kasashen na bukatar hadin kai da kasashen duniya wajen kawo karshen tashe tashen hankulan da yankin na Sahel ke fuskanta.
Tun a shekarar 2014 kasashen na Sahel ke gudanar da aikin hadin guiwa domin tabbatar da tsaro a yankin sakamakon yadda suke fama da mayakan kungiyoyin ta’addanci alámarin da ya haifar da mummunan koma bayan ci gaban alúmma, tsaro da kuma muhalli.
A shekarun baya bayan nan ne dai tashe-tashen hankulan dake addabar yankin arewacin Mali, suka yadu zuwa tsakiyar kasar, da kuma kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.
Wata kididdiga da majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ta nuna cewar hare-haren ‘yan ta’adda da rikicin kabilanci, sun yi sanadin mutuwar kimanin mutane dubu 4, adadin da ya rubanya har sau 5 idan aka kwatanta da shekarar 2016, duk kuwa da kasancewar dakarun wanzar da zaman lafiyar kasashen Afrika, na majalisar ta dinkin duniya da kuma na Faransa a Yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu