Isa ga babban shafi

Idriss Deby zai maida fadarsa zuwa Tafkin Chadi

Shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno ya yanke shawarar mayar da ofishinsa zuwa birnin Bagassola cibiyar lardin Lac a Tafkin Chadi na wani lokaci, domin jagorantar aikin tsara dubarun yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram.   

Shugaban Chadi Idriss Deby Itno
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno BRAHIM ADJI / AFP
Talla

Shugaban ya bayyana hakan ne bayan mummunan harin bazata da Mayakan Boko Haram suka kai kan barikin soji a yankin na tafkin Chadi, wanda ya yi sanadiyar kashe dakarun sojin kasar kusan 100.

Shugaban kasar Chadin Idriss Deby Itno, ya bayyana cewa adadin sojojin har 92 mayakan suka hallaka, bayan da ya ziyarci yankin da lamarin ya auku, inda ya bayyana harin a matsayin mafi muni da kasar ta taba gani a tarihinta.

Rohatanni sun ce, tun a ranar Litinin mayakan na Boko Haram suka kai mummunin harin garin Boma dake lardin Lac, a yankin tafkin Chadi da ya hada iyaka da kasashen Kamaru da Nijar da kuma Najeriya.

Shugaba Idriss Deby da ke jawabi a gidan talabijin din kasar, yace “Mun rasa sojojinmu 92, ciki harda kanana da manyan hafsosi, wasu 47 kuma sun jikkata kuma mun daukosu zuwa Djammena babban birnin kasar”.

Shugaba Deby ya kara da cewa karon farko kenan da sojoji kasar da yawan gaske ke mutuwa loakaci guda,“sojojinmu sun fafata a yake-yake da dama, to amma wannan shine karon farko da muka tafka irin wannan hasara na rayukan dakarun mu a tarihi, don haka zamuyi nazari kan dabarun mu don ganin ba’a sake ganin halin da Boma ya shiga ba”.

Rahotanni sunce, mayakan na Boko Haram da ke da iko da akasari yankin tafkin Chadi, sun iso barikin ne cikin kwale-kwale mai inji, da misalin karfe biyar na yamma, inda suka farma sojojin a bazata.

Majiyar sojin Chadi ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar, mayakan na Boko Haram sunyi awon gaba da tarin makaman yaki, bayan da suka lalata motocin sulke da suka taras a barikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.