Isa ga babban shafi
Nijar-Coronavirus

Nijar ta killace mutane 600 saboda coronavirus

A Jamhuriyar Nijar sabbin alkalumma da mahukunta suka fitar na nuni da cewa adadin wadanda cutar Covid-19 ta kama a kasar sun tashi zuwa 74 bayan da aka samu karin mutane 40 kamar dai yadda aka sanar a daren jiya. A cewar mahukunta tuni cutar ta kashe mutane biyar a kasar, yayin da a karon farko mahukunta suka tabbatar da cewa an gano mutane biyu da suka kamu da cutar a jihar Maradi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Nijar suka killace wasu mutane sama da 600 da gwamnatin Algeria ta tasa keyarsu zuwa Agadez a arewacin Nijar. 

Nijar ta killace mutane 600 saboda coronavirus bayan Algeria ta taso keyarsu zuwa kasar
Nijar ta killace mutane 600 saboda coronavirus bayan Algeria ta taso keyarsu zuwa kasar AFP PHOTO / STR
Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton da Oumarou Sani ya aiko mana daga Agadez

03:00

Nijar ta killace mutane 600 saboda coronavirus

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.