Isa ga babban shafi
Chadi-Boko Haram

Shekau ka mika wuya ko na aika ka lahira- Shugaban Chadi

Shugaban Chadi, Idriss Deby ya bukaci shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da ya mika kansa ko kuma ya kashe shi a mabuyarsa da ke Dikwa.

Shugaban Chadi Idriss Deby Itno tare da dakarunsa a fagen fafatawa da mayakan Boko Haram
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno tare da dakarunsa a fagen fafatawa da mayakan Boko Haram prnigeria
Talla

Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan da shugaba Deby ya jagoranci dakarunsa wajen kaddamar da farmaki kan mayakan Boko Haram tare da kashe mutun 100 daga cikinsu.

A yayin jawabi ga al’ummar Chadi ta kafar talabijin, shugaba Deby ya ce, Shekau na da damar mika wuya a yanzu, in ba haka kuma, a yi amfani da wuta wajen fatattako shi daga mabuyarsa.

Deby ya gargadi Shekau cewa, zai aika shi lahira muddin ya ki mika wuya kamar yadda aka bukace shi ya yi.

A makon jiya ne, dakarun Chadi suka kaddamar da farmaki kan mayakan Boko Haram, farmakin da aka yi wa lakabi da 'fushin Boma' bayan 'yan ta'addan sun yi wa sojojin Chadi kwantar-bauna tare da kashe 92 daga cikinsu.

Shugaba Deby  ya lashi takobin cewa, ba zai taba amincewa da shan kashi ba a wannan gumurzu da mayakan Boko Haram da suka addadi kasashen Tafkin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.