Isa ga babban shafi
Comoros

'Yan Sanda sun sanya jama'a kundunbalar ficewa ta tagogin Masallaci

Jami’an tsaro a Comoros sun harba hayaki mai sa hawaye akan wasu al’ummar Musulmi da suka bijirewa dokar hana taron jama’a wajen gudanar da Ibada a Masallatai, don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Daya daga cikin Masallatan da gwamnati ta rufe a daukacin kasar Comoros, don dakile yaduwar annobar coronavirus.
Daya daga cikin Masallatan da gwamnati ta rufe a daukacin kasar Comoros, don dakile yaduwar annobar coronavirus. AFP
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace an samu arangamar ce a Masallatai guda biyu dake tsibirin Anjoun, abinda ya kai ga jikkatar mutane da dama, cikinsu harda wani da ya karye.

Wani ganau ya ce mafi akasarin mutanen da suka jikkata, na daga cikin wadanda suka rika yin kundunbala wajen ficewa daga cikin Masallatan ta tagogi, a lokacin da jami’an tsaron suka kai musu samame.

Ranar Juma’ar da ta gabata shugaban kasar ta tsibirin Comoros Azali Assoumani, ya sanya hannu kan dokar hana fitar dare, baya ga wadda ta hana zirga-zirga da rana dake aiki.

Har yanzu dai ba a samu rahoton bullar annobar coronavirus ba a Comoros.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.