Isa ga babban shafi
Coronavirus

Kasashen Afrika 15 sun kafa dokar tilastawa mutane sanya takunkumi

Kasashen Afirka 15 sun sanya dokar amfani da kyallen rufe baki da hanci da zummar dakile yaduwar cutar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayukan jama’a a sassan duniya.

Wani fasinja, yayinda ake duba lafiyarsa a filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake birnin Legas a Najeriya. 27/2/2020.
Wani fasinja, yayinda ake duba lafiyarsa a filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake birnin Legas a Najeriya. 27/2/2020. BENSON IBEABUCHI/AFP via Getty Images
Talla

Kasar Kamaru ce ta fara kafa dokar amfani da takunkumin tun daga ranar 9 ga watan Afrilu, yayinda kasashe da dama suka bi sawun ta.

Bayaga Kamaru, kasashen da kawo yanzu suka tilasta amfani da takunkumin rufe baki da hancin sun hada da Angola, Benin, Burkina Faso, Equatoria Guinea, Habasha, Gabon da Guinea da kuma Kenya.

Sauran kasashen sun hada da Liberia, Rwanda, Saliyo, da Zambia, yayinda Najeriya da Afirka ta kudu za su fara aiki da dokar a wannan watan na Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.