Sau 17 aka kaiwa cibiyoyin lafiya hare-hare a 2020 - MDD
Majalisar Dinkin Duniya tace sau 17 dakarun Janar Khalifa Haftar dake kokarin kwace iko da birnin Tripoli a Libya, ke kai hare hare kan asibitoci da kuma cibiyoyin kula da lafiya a cikin wannan shekara.
Wallafawa ranar:
Ofishin Majalisar ya bayyana haka ne bayan harin baya bayan nan da dakarun Haftar suka kai kan babban asibitin Tripoli a ranar alhamis da ta gabata.
Mai Magana da yawun ma’aikatar lafiyar kasar Amin al-Hashemi ya tabbatar da harin wanda yace ya lalata cibiyar kula da lafiyar da sashen yaki da cututtuka masu yaduwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bacin ran ta da yadda dakarun Haftar ke kai hare hare kan fararen hula wanda ke matukar illa ga duk wani yunkuri na sasanta rikicin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu