Isa ga babban shafi
Afrika-Coronavirus

COVID-19: Shugabannin Afrika sun zargi kasashen Turai da karya alkawarin basu tallafi

Shugabannin Afrika sun zargi manyan kasashen duniya da rashin cika alkawuran da suka dauka, na tallafawa nahiyar ta fuskokin basu taimakon kudade da yafe basukan da suke binsu, domin rage musu radadin annobar coronavirus, da ta tagayyara tattalin arzikin Afrika.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara.
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara. John MacDougall/Pool via REUTERS/File Photo
Talla

Shugabannin kasashen da suka hada da na Kenya, Ivory Coast, Saliyo, Senegal da kuma Nijar, sun caccaki manyan kasashen ne a yau talata, yayin wata ganawa da suka yi ta hoton bidiyo, kan halin da ake ciki dangane da yaki da annobar coronavirus.

Shugabannin sun ce a amimakon taimakawa Afrika, kasashe masu arziki sun maida hankali ne kawai wajen zuba biliyoyin daloli zuwa fannoninsu na tattalin arziki da kuma lafiya, domin warkar da raunin da annobar COVID-19 ta yi musu.

Faduwar farashin man fetur da daina samun kudaden shiga daga fannin yawon bude ido, gami da takaituwar harkar sufuri musamman na jiragen sama, na daga cikin manyan batutuwan da suka yi tasiri wajen karya tattalin arzikin nahiyar, duk saboda tasirin annobar coronavirus.

Ganin halin da Afrikan ta shiga ne ya sanya shugabannin nahiyar kira ga kasashe masu arziki gami da hukumomi na kasa da kasa, da su tallafa musu da akalla dala biliyan 100, tare da yafe basukan da ake binsu, domin saukaka musu sahwo kan kalubalen da cutar ta coronavirus ta haifar.

Duk da cewa a waccan lokacin manyan kasashen sun amsa kiran tare da alwashin bada tallafin, har yanzu babu amo ba labarin inda aka kwana, musamman kan batun na yafe basuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.