Isa ga babban shafi
Sudan-ICC

Tsohon shugaban 'yan bindigar Sudan ya mika kansa ga kotun ICC

Kotun Hukunta manyan laifuffuka da ke Haque ta ce yanzu haka tsohon shugaban 'yan bindigar Sudan Ali Kushayb ya fada cikin komar ta, bayan ya gabatar da kan sa domin amsa laifuffukan yaki a Darfur.

Majalisar Dinkin Duniya dai na zargin Ali Kushyap da hannu a rikicin Darfur da ya hallaka mutane kusan dubu dari 3.
Majalisar Dinkin Duniya dai na zargin Ali Kushyap da hannu a rikicin Darfur da ya hallaka mutane kusan dubu dari 3. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Kushayb mai shekaru 63 da aka fi sani da Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman na fuskantar tuhume tuhume 50 da suka shafi laifuffukan yaki da cin zarafin Bil Adama tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004 a Yankin Darfur.

Kotun tace sakamakon bada sammacin kama Kushayb, ya mika kan sa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kuma yanzu haka yana hannun jami’an kotun.

Majalisar Dinkin Duniay ta ce akalla mutane kusan 300,000 suka mutu a rikicin Darfur, yayin da sama da miliyan 2 da rabi suka rasa matsugunin su sakamakon tashin hankalin da ake zargin gwamnatin shugaba Omar Hassan al Bashir da kitsawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.