Isa ga babban shafi
Afrika

Giwaye da dama ne suka mutu a Botswana

Mahukunta a kasar Botswana, sun ce akalla giwaye 300 ne suka mutu daga watan mayu zuwa yanzu a wani gandun daji da ake kira Okavango da ke arewacin kasar.

Hukumomin kasashen Afrika na iya kokarin su don kare Giwaye daga mafarauta
Hukumomin kasashen Afrika na iya kokarin su don kare Giwaye daga mafarauta Tessa Arkwright
Talla

Peter Kat shugaban hukumar kula da wannan gandun daji ke cewa, ga alama an yi amfani da guba ne domin kashe wadannan giwaye.

Wani abu da ba saba ba ne ya faru a dajin, saboda illahirin giwayen sun mutu ne a wani yanki da ake kira Okavango, kuma mafi yawansu an tarar da su ne matattu kwance a kan kirjinsu.

Wannan abun mamaki ne da ke kara tabbatar da cewa ba wai sun mutu ne saboda wani rashin lafiya ba, domin kafin dabba ta mutu saboda wani rashin lafiya, dole ne a ga alamar rama a jikinta.

Har wayau, da a ce wani rashin lafiya ne ke kashe su, to da ko shakka babu matsalar za ta yadu zuwa sassa da dama na kasar Botswana watakila ma da Namibia ko kuma Zimbabwe, domin annoba ba za ta takaita a wani karamin yanki da ke cikin kasar Botswana kawai ba.

A zaton hukumomin gandun dajin, an yi amfani ne da wata guba da ke matukar illa a gare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.