Isa ga babban shafi
Benin

Jamhuriyar Benin ta sake gina gidan tarihin kasar

Jamhuriyar Benin na sake gina gidan tarihin ta domin baiwa 'yan baya damar ganin irin ukubar da jama’a suka sha lokacin mulkin mallaka, a daidai lokacin da kasashen duniya ke watsi da irin wadannan kayan tarihin.

Wajen tarihi a Benin.
Wajen tarihi a Benin. AFP
Talla

A karni na 17 da 18 Turawa Yan mulkin mallaka sun tsare akalla Yan Afirka sama da miliyan guda, maza da mata da kuma yara a Sansanin Ouidah, inda ake amfani da shi wajen sanya su cikin jirgin ruwa a cikin mummunar yanayi.

Ouidah wanda ke da nisan kilomita 40 daga birnin Cotonou, cibiyar tattalin arzikin Jamhuriyar Benin na daya daga cikin manyan tashoshin da akayi amfani da su wajen kwashe bayi zuwa Amurka.

Tarihi ya nuna cewar kasashen Portugal da Birtaniya da Faransa sun yi ta kai farmaki kauyuka suna kama mutanen da suke mayar da su bayi suna tafiya da su tare da hadin bakin Sarakunan Yankin.

Hukumomin Jamhuriyar Benin sun ce sake gina gidan tarihin zai baiwa Yan baya damar sanin irin wahalar da kakanin su suka sha a hannu Turawan mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.