Isa ga babban shafi
Duniya

Bikin ranar samar da abinci ta Duniya

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar samar da abinci ta duniya, wanda ke dauke da taken yadda za’a wadata jama’ar duniya da abinda da za su ci domin cimma daya daga cikin muradun karni.

Wani mutum dauke da buhun abinci agaji
Wani mutum dauke da buhun abinci agaji AFP Photo/Essa Ahmed
Talla

Harkar noma da samar da abinci na daya daga cikin bangarorin dake samun koma baya a kasashe masu tasowa, abinda ya sa kasashe da dama basa iya noma abinda zasu ciyar da al’ummar su.

Noma domin ciyar da al’umma na daya daga cikin manyan sana’oin da jama’ar wannan sashe na duniya suka dogara da shi, kafin matsalolin yau da kullum suka tilastawa wasu mutane watsi da harkar domin rungumar wasu sana’oin da suke ganin zasu fi taimaka musu.

Cigaban zamani ya kuma inganta yadda ake noman wajen samar da na’urori da ake amfani da su da kuma iri da takin zamanin dake bada damar noma manyan gonaki, sabanin yadda aka saba gani a shekarun baya.

Talauci da rashin samun tallafi na hana manoma marasa karfi samun irin wadannan na’urori domin inganta noman da suke, abinda ya sa ayau wasu daga cikin su basa iya noma abinda zasu ci na shekara.

Farfesa Abba Gambo, shugaban tsangayar koyar da noma a Jami’ar Jihar Yobe yayi sharhi kan matsalolin da suke haifar da koma bayan noma da suka hada da rashin daukar tsari guda daga bangaren gwamnati, inda sau tari zaka ga kowacce gwamnati tana zuwa da nata tsari, koda kuwa na wadda ta gada yafi na ta, sai kuma rashin taimakawa manoman.

Masanin yace rashin takin zamani da ingantaccen iri da maganin kwari, abubuwa ne masu matukar tasiri da ya dace ace manoma sun samu kafin damina ta fadi, amma sau tari manoman basa samu sai damina tayi nisa yadda ba za suyi tasiri ba.

Farfesa Gambo yace wata matsala kuma itace har yanzu manoma da dama da fartanya suke noma sabanin cigaban zamani yadda ake amfani da motar noma, wanda shima babbar matsala ce, sai kuma rashin taimakawa manoma wajen saye kayan da suka noma domin sarrafa su ko adana su, abinda ya sa manoman ke tafka asarar dake sanya su watsi da noman.

Masanin ya kuma tabo batun rancen kudi da ake bukatar baiwa manoman domin fadada aikin da suke da zummar ganin manoman sun biya bayan sun yi girbi sun kuma sayar da amfanin gonar su.

Domin shawo kan wadannan matsaloli, Farfesa Gambo ya bada shawarar inganta shirin bada rance da ake baiwa manoma da wuri kafin damuna ta fadi da kuma samar musu iri mai inganci da motar noma da takin zamani.

Samarwa manoma wadannan sinadarin aikin gona, inji masanin, zai taimaka sosai wajen ganin kasashe sun ciyar da kan su musamman ganin irin arzikin da Allah Ya wadata wannan yankin na Afirka ta Yamma wajen samun isashen ruwan sama.

Aminu Sani Sado ya hada rahoto a kai....

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.