Isa ga babban shafi
Najeriya

CPI ta bukaci tsare kafofin yada labarai a Najeriya

Cibiyar yan Jaridu ta Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da tsaro a gidajen yada labarai da Yan Jaridu sakamakon hare haren da aka kai kan kafofin yada labarai guda 5 a birnin Lagos dake kudancin kasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zange dake kokarin kare wani gidan jarida
Wasu daga cikin masu zanga-zange dake kokarin kare wani gidan jarida REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Shugaban kwamitin Cibiyar dake Najeriya Kabir Yusuf yayi mummunar suka kan harin da kuma lalata kadarorin kafofin yada labaran da akayi sakamakon zanga zangar da ta rikide ta zama tarzoma.

Kafofin yada labaran da abin ya shafa sun hada da Jaridar The Nation da tashar talabijin ta Televison Continental da gidajen rediyon Radio Lagos da Eko FM da Traffic FM wadanda aka cinnawa wuta.

Yusuf yace sun amince da yancin gudanar da zanga zanga da bukatar neman kadi amma kuma hari kan kafofin yada labarai abin tada hankali ne da ba zasu amince da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.