Isa ga babban shafi
Mali - Faransa

Sojojin Faransa sun kasashe babban kwamandan Al-Qaeda a Mali

Faransa ta sanar da cewa dakarunta da ke fada da masu ikrarin jihadi a kasar Mali , sun kashe wani babban kwamandan mayakan dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda dake ci gaba da tada kayar baya a yankin sahel.

Sojan rundunar Barkhane na Faransa a yankin Sahel
Sojan rundunar Barkhane na Faransa a yankin Sahel Reuters
Talla

Ministar tsaro faransa uwargida Florence Parly, wace ta yaba da kokarin da sojojin sama da na kasa suka yi, wajen kashe Ba Ag Moussa, da aka bayyana a matsayin kwamandan kungiyar mayakan masu tsatsauran ra’ayin Islama, ta bayyana nasarar a matsayin babban ci gaba ga sojin na faransa a yankin Sahel

An dai hakkake cewa, Ag Moussa wanda aka fi sani da Bamoussa ne, ke da alhakin hare-hare da dama kan sojojin Mali da na kasashen duniya, kuma ana masa kallon daya daga cikin manyan komandojin jihadi a kasar Mali, dake horar da sabbin dakarun da aka dauka.

A watan yunin da ya gabata, dakarun na Frarnsa sun hallaka Abdelmalek Droukdei, shugaban Al Qaeda reshen kasashen yankin sahel, mai alaka da kungiyar mayakan GSIM.

An dai bayyana Ag Moussa a matsayin tsohon sojan kasar Mali mai mukamin Kanal, kafin rikedewa ya zama daya daga cikin manyan yan mayakan dake ikararin jihadi a kasar

Idan dai ba a manta ba , Mali da ta dade tana faman tashe tashen hankulan kungiyoyin yan ta’ada da na masu ikrarin jihadin islama, tun cikin shekarar ta 2012 al’amarin da ya yi sanadiyar rasa dubban rayukan al’ummar kasar, sojojin Farasa da kuma na MDD, a ya yin da rikicin ya shafi kasashen Burkina Faso da jamhuriyar Niger dake makwabtaka da Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.