Isa ga babban shafi
Najeriya

Dokar zabe ta hanna yan Najeriya miliyan guda kada kuri'a-Mahmud

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu yace akalla Yan kasar sama da miliyan guda ne da suka kai mizanin yin zabe aka hana su shiga zaben da ya gabata saboda dokar da ake amfani da ita.

Wasu daga cikin masu zabe a Najeriya
Wasu daga cikin masu zabe a Najeriya STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Yayin da yake jawabi ga kwamitin Majalisar Dattawa dake tantance shi domin yin wa’adi na biyu, Farfesa Yakubu yace dokar da ake aiki da ita yanzu bata bada damar kada kuri’a ga mutanen da suka sauya wuri daga inda suka yi rajista ba, abinda ke hana su kada kuri’a da zaran lokacin zabe ya same su a wasu wurare na daban.

Shugaban yace wannan doka ta kuma hana mutanen dake aiki na musamman irin su jami’an hukumar zaben da yan jaridu da jami’an tsaro da kuma masu sanya ido dake tafiya wasu wurare damar kada kuri’un su lokacin gudanar da zaben.

Farfesa Yakubu yace Hukumar ta dauki akalla ma’aikata miliyan guda lokacin zaben kasa da akayi bara, abinda ya sa dokar da ake amfani da ita ta hana su kada kuri’a.

Shugaban Hukumar ya bukaci yiwa dokar zabe gyaran fuska domin ganin an baiwa jama’a da dama damar sauke nauyin dake wuyar sun a zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.