Isa ga babban shafi
Faransa

Yan Sanda sun azabtar da wani dan Jarida a Paris-RSF

Kungiyar yan jarida ta Reporter Sans Frontieres ta kalubalanci yada yan Sanda suka yi amafani da karfi tareda cin zarafin wani dan jarida dan kasar Syria a lokacin zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tsaro dake haramta daukar jami’an tsaro hoto yayin gudanar da ayyukan su a jiya asabar.

Masu zanga-zangar adawa da dokar hana daukar yan sanda hoto yayin aikinsu
Masu zanga-zangar adawa da dokar hana daukar yan sanda hoto yayin aikinsu REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

‘Yan sandan Faransa sun yi arangama da Dan jaridar mai suna Ameer AL Halbi mai shekaru 24 dan kasar Syria dake aiki da Mujalar Polka Magazine da kamfanin dilancin labaren Faransa.

Kungiyar ta bakin sakatary ta Christophe Deloire ta bayyana takaicin ta,cewa kasa kamar Faransa bai dace masu aikin jarida su dinga fuskanatar irin wadanan matsaloli ba.

Mista Deloire da sunan kungiyar ya jajintawa Ameer Al Halbi.

Rahotanni sun ce an gudanar da zanga zangar a fadin kasar baki daya, inda a birnin Paris kawai akayi kiyasin mutane sama da dubu 46 da suka shiga zanga-zangar.

Hotan biyon da aka yada na Yan Sandan suna dukar wani mai shirya wakoki Michel Zickler ya haifar da suka mai zafi kan jami’an, ciki harda shugaba Emmanuel Macron wanda ya bayyana shi a matsayin abin kunya a gare su.Tsohon Shugaban kasar Francois Hollande yayi Allah wadai da wannan tsari da hukumomin kasar ke shirin aiwatar ,Hollande na fadar haka ne a yayin wata ganawa da jaridar Le Dimanche ta kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.