Wakilai 120 daga majalisar Libya suka cimma matsaya A Morocco
Wakilai 120 daga zauren majalisar Libya ne suka cimma matsaya don kawo karshen rikicin kasar a wani taron sassanta shugabanin kungiyoyi dake fada da juna a Libya da ya gudana kasar Morocco.
Wallafawa ranar:
Kusan shekaru biyu kenan da majalisar ta kasa gudanar da taron ta,tun bayan da Libya ta fada cikin rikici bayan mutuwar tsohon Shugaban ta Mohammar Khadafi a shekara ta 2011.
A watan Oktoba ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyoyin biyu dake fada da juna a Libya, a wannan karo bayan share kusan kwanaki biyar ana tattauanwa tsakanin bangarorin a Tabger dake Morocco,123 daga cikin wakilai 180 dake zauren majalisa suka amince da rattaba hannu a wannan takardar samar da zaman lafiya da kuma kawo karshen kalaman nuna kyama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu