Isa ga babban shafi
Afrika

Harin ta'addanci a Somalia ya hallaka mutane 16

A Somalia, mutane da dama suka jikkata biyo bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai tsakiyar Somaliya cikin daren jiya juma’a, inda aka bayyana mutuwar mutane 16.

Jami'a tsaron Somalia a harabar wani Otel da aka kai harin  kunar bakin wake
Jami'a tsaron Somalia a harabar wani Otel da aka kai harin kunar bakin wake REUTERS/Feisal Omar
Talla

Dan kunar bakin waken ya tarwatsa kan sa ne a harabar filin wasa, wurin da ake dakon Firaministan kasar Rooble Mohammed Hussein, inda aka samu mutuwar manyan hafsan sojan kasar uku.

A cewar wani babban hafsan sojan kasar kanal Ahmed Dahir ,dan kunar bakin wake na da niyar kai hari kan wasu manyan hafsan sojan kasar dake cikin tawagar firaministan kasar.

Wani babban hafsan sojan kasar ta wayar talho ya sheidawa kamfanin dilancin labaren faransa na Afp cewa an samu karin mutane da suka rasa rayukan s u a wannan hari na jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.