Isa ga babban shafi
Afrika

Dan adawan Chadi Kebzago na fuskantar tuhuma

A Chadi, Ministan shara’a ya mika wasikar gurfanar da tsohon jagoran yan adawa kuma dan majalisa Saleh Kebzago ga Majalisar kasar.Ana tuhumar Kebzago da furta wasu kalamai da basu dace ba.

Saleh Kebzago,Dan Majalisa ,tsohon jagoran yan adawa a Chadi
Saleh Kebzago,Dan Majalisa ,tsohon jagoran yan adawa a Chadi France24
Talla

Wasikar da ta shiga hannun yan majalisun daga ofishin Ministan shara’ar kasar Chadi, na bayyana tuhumar da ake yiwa tsohon jagoran yan adawa Saleh Kebzago, dan siyasar dake adawa da Shugaban kasar Idris Deby zai gurfana gaban kotu.

Ana dai tuhumar sa ne da furta kalaman tunzura jama’a ga bore tareda nuna kabilanci a yayin taron siyasa da wasu manoman dake fada da makiyaya.

Ranar 22 ga watan disemba ne dan siyasar ya furta wadanan kalamai, ana dai dakon zaman majalisa wacce za ta bayar da amincewar ta don tisa keyar Saleh Kebazago gaban alkalai.

Wasu rahotani na nuni cewa dan siyasar a wancan lokaci yayi tattaki zuwa yankin Tandjile, wurin da aka fuskanci fada tsakanin makiyaya da manoma.Yankin da aka fuskanci rikicin da ya haddasa mutuwar mutane a lokacin.

Da jimawa kungiyoyi suka bukaci gwamnati ta dau mataki a kai.

Kalo ya koma bangaren majalisa ,inda ake sa ran yan Majlisa za su bayar da ta su matsaya domin ganin an rusa tuhumar da ake yiwa Kebazgo ko kuma ya gurfana gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.