Isa ga babban shafi
Faransa-Chadi

Faransa na tattaunawa da Chadi kan yaki da ayyukan ta'addanci a Sahel

Firaministan Faransa, Jean Castex ya fara tattaunawa da shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno kan yadda za a sake karfafa yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.

Firaministan Faransa Jean Castex yayin tattaunawarsa da shugaba Idris Deby Itno na Chadi.
Firaministan Faransa Jean Castex yayin tattaunawarsa da shugaba Idris Deby Itno na Chadi. France24
Talla

Jean Castex wanda yanzu haka ke ziyara a kasar ta Chadi inda ya yi bikin sabuwar shekara tare da dakarun Faransa da ke yaki da ta’addanci a cikin rundunar G5 Sahel, ya shaidawa manema labarai a cewa baza su gaza ba wajen tallafawa kasashen yaki da matsalar tsaron da ta dabaibaye su.

A cewar Firaministan na Faransa ya yi tattaunawa mai matukar muhimmancin da Idris Deby wanda ya bashi kwarin gwiwa a yakin da kasarsa ke yi da ayyukan ta’addanci.

Shugabannin biyu wadanda suka yi ganawa ta musamman a Amdjarass kan iyakar Chadin ta gabashi da ta yi gab da kasar Sudan, sun tattaunawa batutuwan da suka shafi sake hada karfi tsakanin kasashen Sahel da na yankin tafkin Chadi don kammala yakar ‘yan ta’addan da ke barazana ga tsaronsu.

Tun a shekarar 2013 Faransa ta shiga yaki da ayyukan ta’addanci a yankin na Sahel musamman kasar Mali da tun a wancan lokaci ta fara fuskantar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi, wanda suka fadada hare-harensu zuwa kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

Wasu bayanai sun nuna yiwuwar shugaba Deby ya kai wata ziyara Faransa don tattaunawa da shugaba Macron a watannan, haka zalika akwai yiwuwar taron kolin tsaro tsakanin kasashen na G5 Sahel a watan da muke ciki na Janairu ko kuma Fabarairun da ke gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.