Isa ga babban shafi
Afrika

Majalisar dinkin duniya ta kawo karshen aikin dakarunta a Sudan

Majalisar dinkin duniya ta kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiyar da dakarunta ke yi a yankin Darfur dake Sudan, bayan shafe shekaru 13.

Daya daga cikin motocin dakarun wanzar da zaman lafiya a Darfour dake yankin  Djebel Marra a Sudan
Daya daga cikin motocin dakarun wanzar da zaman lafiya a Darfour dake yankin Djebel Marra a Sudan ASHRAF SHAZLY / AFP
Talla

Sai dai Kakakin rundunar wanzar da zaman lafiyar, Ashraf Eissa ya shaidawa kamfanin dillacin labarai an AFP cewar sai a karashen watan Yunin shekara 2021ne za su soma janye dukkanin dakarun da sauran ma’aikatar rundunar sojin majalisar dinkin duniyar da aikinta ya kare a ranar Alhamis 31 ga watan Disamba 2020.

Akalla mutane dubu 300 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekarun da aka shafe ana gwabza yaki a yankin Darfur, yayin da wasu miliyan 2 da dubu 500 suka rasa muhallansu, kamar yadda alkaluman majalisar dinkin duniya suka nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.