'Yan bindigar ADF sun kashe fararen hula 25 a Jamhuriyar Congo
Akalla mutane 25 sun mutu a wani hari kan al’ummar yankin Beni na Arewacin Kivu a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, farmakin da mahukuntan kasar suka dora alhakinsa kan ‘yan bindigar kungiyar ADF da suka yi kaurin suna wajen kisan fararen hula a shekarun baya-bayan nan.
Wallafawa ranar:
Babban jami’in da ke kula da yankin na Beni Donat Kibuana ya ce an gano gawarwakin mutanen 25 ne lokacin da Soji ke bin sahun wasu mayakan ADF zuwa maboyarsu a daren jiya Alhamis.
A cewar jami’in, lamarin ya faru ne a kauyen Tingwe mai tazarar mil biyar da kauyen Eringeti yankunan da mayakan na ADF ke yawaita kai farmaki tare da hallaka tarin fararen hula.
Sai dai shugaban kungiyoyin fararen hula a yankin na Tingwe, Bravo Mohindo Vukulu ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa adadin mutanen da suka mutu a farmakin ka iya zarce 30 la’akari da yadda ake ci gaba da laluben wasu gawarwakin.
Mr Vukulo ya ce mutanen su na tsaka da shirye-shiryen bikin sabuwar shekara ne ‘yan bindigar na ADF suka yi musu dauki dai-dai tare da yi musu kisan gilla, wanda zuwa yanzu ba a kammala gano adadinsu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu