Zan kawo gyara ta fuskar tsaro- Buhari
Matsallar cin zarafin da ake zargin jami’an tsaron Najeriya na ci gaba da ciwa shugaban Najeriya tuwo a kwariya, Shugaba Muhammadu Buhari ya dau alkawali kawo gyara inda yake cewa masu zanga-zangar EndSARS da ta fi muni a jihar Lagas na dada nuni irin matsaloli da jama’a ke fuskanta,ya zama wajibi gwamnatin sa ta saurari koken mutan kasar ta fuskar tsaro da kuma kare hakkokin jama’a.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Buhari na magana ne a yayin da yake gabatar da jawabin sabuwar shekara gay an kasar kamar yada jaridar Premium Times dake Njaeriya ta ruwaito.
Ya zuwa yanzu kungiyoyi daga ciki da wajen kasar sun zura idanu suna dakon sakamakon binciken da sama da jihohi 20 na kasar suka kaddamar biyo bayan zargin da ake yiwa jami’an tsaro na azabatar da farraren hula a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu