Fada ya barke tsakanin yan Sanda da mazaunan Dakar
‘Yan sandan Senegal sun yi arrangama da wani gungu daga cikin daruruwan matasan da suka fantsama kan titunan yankin Ngor dake birnin dakar inda suke zanga-zangar adawa da matakan takaita walwalar da gwamnati ta kafa don dakile yaduwar annobar coronavirus ciki har da hana fitar dare.
Wallafawa ranar:
Matasan sun yi ta kona tayoyi gami da kafa shingayen hana zirga-zirga a kan tituna yayin boren abinda ya sanya ‘yan sanda amfani da karfi wajen kokarin tarwatsa su.
Ranar laraba shugaban Senegal Macky sall ya ayyana dokar ta baci a wasu yankunan kasar ciki har da birnin Dakar, inda ya kafa dokar hana fitar dare daga karfe 9 zuwa 5 na safiya, don dakile yaduwar annobar Korona.
Wasu kasashen na Afrika na dab da yi koyi da kasar ta Senegal a wannan shiri na takaita zirga-zirgar jama'a sabili da cutar Coronavirus dake ci gaba da lakume rayukan jama'a a Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu