Isa ga babban shafi
Afrika

Zan kasance na farko da za a yiwa allurar Coronavirus - Buhari

Gwamnatin Najeriya tace shugaba Buhari da mataimakinsa farfesa Osinbanjo gami da wasu mukarraban gwamnatin zasu kasance mutane na farko da za su karbi alluran rigakafin cutar coronavirus, kuma za a nuna hakan kai tsaye ta kafar talabijin domin kwantarwa da al’ummar kasar hankali dangane da ingancin maganin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@BashirAhmaad
Talla

Najeriya za ta karbi alluran riga-kafin coronavirus na Pfizer da Biontech akalla dubu 100 nan da karshen watan Janairun da muke ciki.

Babban Darekta a hukumar kula da Kiwon Lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib ya bayyana haka a yayin jawabinsa ga Kwamitin Yaki da Cutar Corona na shugaban kasa.

Shu’aibu ya kuma ce, Najeriya mai yawan al’umma fiye da miliyan 200, na sa ran samun alluran-riga-kafin miliyan 42 a zango na biyu.

A bangare guda, gwamnatin Najeriyar ta ce, ta fara tattaunawa da China game da samun alluran riga-kafin cutar.

Wannan na zuwa ne yayin da Najeriyar ta samu adadin masu kamuwa da cutar mafi muni da ta taba gani cikin kwana daya, inda mutane da dama suka harbu a jihohin kasar 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.