Isa ga babban shafi
Coronavirus-Afrika

CDC ta bukaci gaggauta yiwa Afirkawa rigakafin Coronavirus

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Afrika CDC ta ce dole ne kasashen nahiyar su kara kaimi wajen samarwa al’ummominsu rigakafin Coronavirus cikin sauri ganin yadda cutar ke ci gaba da kisa a bangare guda kuma aka fara samun wasu nau’ikanta masu matukar hadari.

Tarayyar Afrika AU ta sanar da shirin tallafawa kassahen da basu da karfin iya wadata al’ummominsu da alluran rigakafin ta Coronavirus.
Tarayyar Afrika AU ta sanar da shirin tallafawa kassahen da basu da karfin iya wadata al’ummominsu da alluran rigakafin ta Coronavirus. NIAID
Talla

Shugaban hukumar ta CDC John Nkengasong ya ce rigakafin Coronavirus bai kamata ya zama irin na kyanda ko polio da kasashen na Afrika ke jan kafa wajen yinsa ba, kamata ya yi ayi shi cikin gaggawa don kare al’umma.

A jawabinsa yayin wani taron manema labarai Mr Nkengasong ya ce sam shugabannin kasashen na Afrika basu da wata hujja da za su fake da ita wajen kin yiwa jama’arsu rigakafin cutar.

A Larabar da ta gabata ne kungiyar Tarayyar Afrika AU ta sanar da shirin tallafawa kassahen da basu da karfin iya wadata al’ummominsu da alluran rigakafin ta Coronavirus, a wani yunkuri na tabbatar da wadata alluran a sassan Nahiyar.

Akalla alluran rigakafin miliyan 50 ake saran AU ta karba daga watan Aprilu zuwa Yunin shekarar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.